Dole a bayyana mana lafiyar Buhari-PDP

Dole a bayyana mana lafiyar Buhari-PDP

Jam’iyyar PDP mai adawa tace dole a sanar da ‘Yan Najeriya cutar da ke damun shugaban kasa Muhammadu Buhari. A Ranar Juma’a ne dai Buhari ya dawo kasar daga Landan.

Dole a bayyana mana lafiyar Buhari-PDP

Dole a bayyana mana lafiyar Buhari-PDP

Bangaren PDP da ke karkashin Sanata Ahmed Makarfi ta bayyana cewa ya kamata a sanar da ‘Yan Najeriya yanayin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Mai magana da bakin Jam’iyyar Dayo Adeyeye ya bayyana haka bayan shugaban ya dawo.

Jam’iyyar PDP mai adawa tace tana taya kowa murnar dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan yayi doguwar jinya a Birnin Landan. A Ranar Juma’a ne dai Buhari ya dawo kasar daga Landan inda yayi kwanaki 50 wajen ganin Likita.

KU KARANTA: Ban taba irin wannan rashin lafiyar ba - Buhari

Jam’iyyar tayi addu’a Ubangiji ya karawa shugaban kasar lafiya sannan kuma tace ya kamata a rika bayyanawa ‘Yan kasa abin da ke faruwa game da sha’anin rashin lafiyar shugaban kasar. Jam’iyyar ta yabawa kokarin da Mataimakin shugaban kasar Farfesa Osinbajo yayi a lokacin.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari dai yace bai taba fama da rashin lafiyar da ta kai wanda yayi ba wannan karo tun da yake karami. Shugaba Buhari yace har karin jini aka rika yi masa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana murnar dawowar Shugaba Buhari a Daura

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel