Ba zan iya tuna lokaci na karshe da aka sa mun jini ba – Buhari

Ba zan iya tuna lokaci na karshe da aka sa mun jini ba – Buhari

- Shugabna kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai iya tuna lokacin karshe da aka sanya masa jini ba

- Shugaban kasar ya kara da cewa babban kalubalen da ke fuskantar tsarin kiwon lafiyar Najeriya shine kula da kai

- Ya kuma gode ma yan Najeriya kan addu’o’in su gare shi a lokacin da ya tafi hutun ganin likita

Ba zan iya tuna lokaci na karshe da aka sa mun jini ba – Buhari

Akwai alamomin cewa an sanya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari jini a yayinda yake kasar Ingila kan kula da lafiyar sa.

A yayin da shugaban kasar ke magana da manyan jami’an gwamnati a ranar Juma’a, 10 ga watan Maris bayan dawowar sa ya ce ba zai iya tuna lokaci na karshe da aka sanya masa jini ba a rayuwar sa, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Hausawa sun bar Ile-Ife bayan rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama

Yayinda yake magana kan kalubalen da ya fuskanta a lokacin hutun sa shugaban kasa Buhari ya ce: “Ba zan iya tuna lokaci na karshe da aka sanya mun jini ba; gaskiya ba zan iya tuna wa ba, zan dai iya cewa a cikin shekara ta na 70.”

Yayinda shugaban kasar ya bayyana babban kalubalan da ke fuskantar tsarin lafiyar Najeriya, bai dai ce kowannan bane ya yi sanadiyan rashin lafiyar da yayi ba.

Ya ce: “Ina ganin daya daga cikin muggan abubuwa shine shan magani da kai. Bamu yarda da likitocin mu ba sannan mun fi yarda da kawunan mu.”

“Inda na ziyarta, sukan sha magani ne idan akwai bukatar yin haka. Ba sa hadiyan komai da komai,” inji Buhari.

“Na samu lafiya sosai a yanzu; babu mamaki akwai bukatar wasu abubuwa da zasu biyo baya a cikin wasu makonni,” cewar sa.

Ya ci gaba da yaba ma mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan kokarinsa gurin kula da al’amuran kasar yayinda ya tafi hutu.

KU KARANTA KUMA: An ceto ma’auratan Abuja da aka yi garkuwa da su (HOTUNA)

A halin yanzu, shugaban kasa Buhari ya shawarci yan Najeriya da su tsaya a inda suke don yi masa da Najeriya addu’a a maimakon zuwa Abuja don yi masa sannu da zuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya a ranar Juma’a, 10 ga watan Maris, bayan hutun ganin likita a kasar Ingila.

A lokacin da yayi tafiya, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasar Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel