Abin da Buhari ya fada mani da na ke rike da kasar – Osinbajo

Abin da Buhari ya fada mani da na ke rike da kasar – Osinbajo

– Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya bayyana yadda suka yi da Buhari

– Osinbajo yace Buhari ya fada masa yayi duk abin da ya dace lokacin da yake Landan

– Farfesa Yemi Osinbajo ya godewa shugaba Muhammadu Buhari

Abin da Buhari ya fada mani da na ke rike da kasar – Osinbajo

Abin da Buhari ya fada mani da na ke rike da kasar – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya godewa shugaba Muhammadu Buhari game da damar da ya ba sa na rike kasar a yayin da shugaban ya tafi Kasar Birtaniya domin ya ga Likita na tsawon lokaci.

Farfesa Osinbajo ya bayyana yadda suka yi da shugaba Buhari lokacin yana rikon kwaryan kasar. Osinbajo yace shugaba Buhari ya fada masa ya daina tuntubar sa a waya kafin ya aikata wani abu. Shugaba Buhari ya fadawa Osinbajo ya je ya aikata duk abin da ya ga ya dace da kasar.

KU KARANTA: Ban taba ciwo irin wannan ba - Buhari

Shugaban kasar dai ya dawo Ranar Juma’a inda yace bai taba fama da rashin lafiyar da ta kai wanda yayi ba wannan karo tun yana karami. Shugaba Buhari yace har karin jini aka rika yi masa. Osinbajo dai ya bayyana cewa ya gamu da kalubale wajen mulkin kasar don kuwa ba abu ne mai sauki ba.

Shi kuma Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kira ‘Yan Najeriya su cigaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a domin ya samu sauki. Gwamnan yace akwai aiki na gyaran kasar a gaban shugaba Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana murnar dawowar shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel