An yi fada tsakanin tsohon Gwamnan CBN da wani tsohon Gwamna

An yi fada tsakanin tsohon Gwamnan CBN da wani tsohon Gwamna

Sai ga shi an buge da cacar baki tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomole da kuma tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Farafesa Charles Chukwuma Soludo.

An yi fada tsakanin tsohon Gwamnan CBN da wani tsohon Gwamna

An yi fada tsakanin tsohon Gwamnan CBN da wani tsohon Gwamna

An yi ‘yar rigima da musayar kalamai tsakanin Adams Oshiomole tsohon Gwamnan Jihar Edo da kuma Farfesa Charles Soludo tsohon Gwamnan CBN na kasa. Soludo ya zargi Gwamnatin Buhari da jagwalwala tattalin arzikin Najeriyda inda Oshiomole ya maida masa da martani.

A wajen wani taro game da tattalin arzikin Najeriya tsohon tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Farafesa Charles Chukwuma Soludo yace har yanzu ba a ga wani canji game tattalin arziki musamman wajen kasafin kudin kasa ba. Soludo yace rashin aikin yi da farashin dala da kuma tsadar kaya na ta kara hawa sama a Gwamnatin Buhari.

KU KARANTA: 'Yan Jihar Enugu na murnar dawowar Buhari

Sai dai tsohon Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomole a karkashin APC yayi wuf ya maida martani ga Farfesa Soludo inda ya soki aikin da yayi a Bankin kasar na CBN. Oshiomole yace an bayyana masa yadda Soludo ya azurta wasu aminan sa a banki bayan ya karya farashin dala a wancan lokaci.

Farfesa Soludo kuwa dai yace Oshiomole na kokarin kauda hankalin Jama’a ne don haka ya koma sheka karya. Shi ma dai haka Soludo ya maidawa tsohon Gwamnan martani a taron.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel