Hausawa sun bar Ile-Ife bayan rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama

Hausawa sun bar Ile-Ife bayan rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama

Sakamakon wani rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama da raunata wasu a Ile-Ife, jihar Osun, Hausawa dake zaune a garin sun fara barin garin.

An rahoto cewa daruruwan Hausawa na barin garin a tawaga daban-daban, ta motocin haya.

Yayinda wasu ke daukar hanyar Ilesa, wasu su bi hanyar Akure inda zasu iya samun motoci da zasu tafi Arewa kai tsaye.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa mutanen Hausawa sunyi ikirarin cewa mutanen su ne kawai suka mutu, sakamakon harin da yan iska suka kai masu da muggan makamai wanda suka hada da bindigogi, adduna da sauran su.

Hausawa sun bar Ile-Ife bayan rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama

Rahoto ya nuna cewa Hausawa sun fara tserewa daga Ile-Ife a ranar Laraba lokacin da rikicin yayi muni sannan kuma sun tsere kungiya-kungiya a yammacin ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta nuna godiya ga yan Najeriya yayinda mai gidanta ya dawo

Daya daga cikin shugabannin Hausawa, Afobaje din al’umman Hausawa dake Ile-Ife, Alhaji Malami Nasidi, ya fada ma Saturday Sun cewa akwai bukatar mutanen sa su bar garin cikin gaggawa don tsere ma sabon hari.

A cewar sa, basu da gurin bacci, inda ya kara da cewa shi da iyalinsa da sauran wadanda rikicin ya cika dasu a waje suke bacci kuma babu tabbaci a kan tsaron su.

Ya ce: “Akwai bukatar mu tafi a yanzu mutanen mu nata kiran mu kan mu dawo gida sannan bamu da zabi da ya wuce tafiya har sai zaman lafiya ya dawo gaba daya.”

Wani da ya tsira, Mustapha Hassan daga Zaria yace wadanda abun ya afku da su basu da wani zabi da ya wuce koma wa Arewa tunda an hallaka gidajen su, an bar su sun zama marasa galihu.

KU KARANTA KUMA: Kalli kyakkywan kyauta Aisha Buhari ta ba maigidanta da ya dawo (Hotuna, Bidiyo)

Wani da ya tsira, Mustapha Nadabo ya ce: “Tun kwanaki uku da suka wuce lokacin da fadan ya fara sun kashe mutanen mu da yawa, rigar dake jikina a yanzu shine abunda ya rage mun kawai. Na rasa komai. Bani da zabin da ya wuce komawan Arewa inda na fito.”

Wani shugaban Hausawa, Alhaji Buhari Halum, yay i korafi a kan harin, cewa mutanen Hausawa a Ife sunyi zaman lafiya da hadin kai tare da Yarbawa tsawon shekaru da dama sannan yayi mamakin dalilin da yasa daga baya suka dauki makamai a kan sub a tare da da duba dogon dangantakar dake tsakaninsu ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel