EFCC ta maka Andrew Yakubu kotu, ta tuhume shi da manyan laifuka 6 (Karanta)

EFCC ta maka Andrew Yakubu kotu, ta tuhume shi da manyan laifuka 6 (Karanta)

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annadi watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) sun maka tsohon manajan NNPC Andrew Yakubu a kotu suna tuhumar sa da laifuka 6.

EFCC ta maka Andrew Yakubu kotu, ta tuhume shi da manyan laifuka 6 (Karanta)

EFCC ta maka Andrew Yakubu kotu, ta tuhume shi da manyan laifuka 6 (Karanta)

Wannan tuhuma ta laifuka 6 na dauke ne a cikin wata kara da hukumar ta shigar a gaban kotun tarayya dake Abuja a ranar Alhamis 9 ga watan Maris.

Laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa dai sun hada da kin bayyana kadarorin sa da bai yi ba da kuma tara makudan kudade a gida.

KU KARANTA: Yan majalisa zasu tuhumi Osinbajo

A farkon satin da ya gabata ne dai Tsohon manajan rukunin kamfanonin mai na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC), Andrew Yakubu ya shigar da kara yana tuhumar EFCC da gwamnatin tarayya.

Andrew Yakubu ya maka EFCC din ne tare da gwamnatin tarayya inda yake kalubalantar sama shin da sukayi tare da abun da ya kira kwace mashi kudin sa a garin Kaduna.

A karar da ya shigar a gaban babbar kotun tarayya dake a garin Abuja, Lauyan da ke kare shi Ahmed Raji (SAN) ya shaidawa kotun cewa suna bukatar kotun ta tilastwa EFCC da gwamnatin tarayya su ba wanda yake karewa N1biliyan domin sun tozarta shi sannan kuma su fito cikin jarida su bashi hakuri.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel