Ba’a nada ni shugaban Kastam domin in sa Inifam ba – Hameed Ali ga Majalisan dattawa

Ba’a nada ni shugaban Kastam domin in sa Inifam ba – Hameed Ali ga Majalisan dattawa

Kwantrola Janar na hukumar Kastam, Kanal Hameed Ali ya mayar da martini ga majalisar dattawan Najeriya inda yace ba’a nada shi domin sanya Inifam ba.

Ba’a nada ni shugaban Kastam domin in sa Inifam ba – Hameed Ali ga Majalisan dattawa

Ba’a nada ni shugaban Kastam domin in sa Inifam ba – Hameed Ali ga Majalisan dattawa

Yayinda yake Magana akan gayyatan da majalisar dattawa tayi masa a ranan Laraba, 9 ga watan Maris, sanye da Inifam, Ali ya fadawa gidan talabijin TVC cewa an nada shi domin yin aiki ne. yace shin Inifam ne zai yi aikin ko mutumin?.

KU KARANTA: An fara gyaran jirgin saman Abuja

Yace: “ Har yanzu ban samu wasikar gayyat ba, idan akabi tsari da ka’idoji, zan bayyana gaban majalisar dattawa.”

''Shin ina aikina ko banayi? , A tunani na, abin da ya kamata majalisar ta damu da shi kenan."

Sanata Dino Melaye a ranan Alhamis ne ya gabatar da zancen cewa majalisar dattawa ta gayyaci Kanal Hameed Ali kuma wajibi ne ya zo sanye da Inifam din Kastam.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel