Allah ne ya saka wa Jama’a son Buhari Inji wani Malami

Allah ne ya saka wa Jama’a son Buhari Inji wani Malami

Allah ne ya saka wa Jama’a son Buhari Inji wani Malami

Allah ne ya saka wa Jama’a son Buhari Inji wani Malami

Wani Babban Malamin addini a Zaria yayi kira da ‘Yan Shi’a su tuba bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau.

Babban Malami Dakta Sa’eed Muhammad Yunus da ke Zariya a yau inda yake huduba a masallacin ITN da ke Zangon-Shanu Zaria yayi farin cikin dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma yi wani kira ga ‘Yan Shi’a.

Malamin yayi kira da Jama’a su guji irin abin da suke furtawa a bakunan su domin akwai hisabi a lahira. Sannan dai Limamin yayi kira da ‘Yan Shi’a da suka rika kullace-kullace domin ka da Buhari ya dawo su tuba su karbi musulunci bayan Allah ya nuna masu iko.

KU KARANTA: An koro wani Dan Najeriya daga Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari ya iso gida lafiya inda ya gana da iyalin sa da sauran Jama’a na gidan sa da Gwamnati. Shugaban kasar yayi godiya ga ‘yan kasar da suka sa shi a addu’a inda yace kuma zai cigaba da bakin kokarin sa wajen gyara Najeriya

Limamin ya bayyana cewa Ubangiji ne kurum ne ya sakawa ‘Yan Najeriya kaunar Muhammadu Buhari ya kuma kira ‘yan kasar gaba daya su mara masa baya wajen gyara kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel