YANZU-YANZU! Darajar Naira ta sake faduwa bayan dawowar Buhari

YANZU-YANZU! Darajar Naira ta sake faduwa bayan dawowar Buhari

Labaran da ke shigo mana yanzu suna nuni da cewa darajar Naira ta sake faduwa a yau din nan Juma'a 10 ga watan Maris awowi kadan bayan dawowar shugaba Buhi daga Landan.

YANZU-YANZU! Darajar Naira ta sake faduwa bayan dawowar Buhari

YANZU-YANZU! Darajar Naira ta sake faduwa bayan dawowar Buhari

Rahotannin da muka samu daga kasuwannin canji na cikin gida na nuni da cewa a yau din darajar Naira ta fadi zuwa N463 a kan kowace dala a maimakon N462 da aka saida ta a jiya Alhamis 9 ga watan Maris.

Haka zalika an saida kudin Pounds na kasar Birtaniya a kan N555 mai makon N550 da aka saida shi kafin dawowar shugaban.

KU KARANTA: Kungiyar fulani ta gargadi Fayose game da Buhari

Mai karatu dai zai iya tunawa cewa, Babban Bankin Najeriya yace zai ci gaba da samar da daloli cikin kasuwar hada hadar kudade har sai darajar Naira ta dawo.

Yan haka dai babban Bankin Najeriya yana ci gaba da fitar da miliyoyin Daloli zuwa kasuwar hada-hadar kudade, inda a wannan makon ya sako Dala miliyan 367 don cimma bukatun ‘yan kasar.

A makon da ya gabata ma sai da babban Bankin ya sako Dala miliyan 180 ranar Litinin da kuma karin wasu miliyoyi har 350 a ranar Juma’a, don baiwa Naira damar samun daraja a fadin kasar.

Daraktan hulda da jama’a na babban bankin Najeriya, Dakta Isaac Okorafo, yace a duk lokacin da suka saki daloli masu yawa Naira na ‘kara samun daraja.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel