Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

- Labaran da muke samu yanzu yanzu suna nuni da cewa garin Daura dake zaman mahaifar Shugaba Buhari ya kaure murana sakamakon dawowar shugaban da safiyar yau.

- An dai dandazon jama'ar garin da ma masoya da dama daga makobtan garin sun yi dandazo a filin sukuwar garin dake gaban fadar sarkin na garin dama sauran manyan tituna na garin.

Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

Haka zalika ma masu babura da motoci suna ta karakaina a kan titunan garin domin nuna murnar su da dawowar shugaban.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a da misalin karfe 4 a.m, bayan kwanaki 51 da barin kasar don hutun ganin likita.

Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

Yadda jama'ar garin Daura suka gudanar da murnar dawowar shugaba Buhari (Hotuna)

A cewar jaridar Thisday, sakamakon rufe filin jirgin saman Abuja an shirya saukar jirgin sa a filin jirgin Kaduna a safiyar ranar Juma’a, bayan shawarar da aka yanke na dawo dashi a jirgi mai saukar ungulu zuwa fadar shugaban kasa, Abuja.

Majiyar ta kuma bayyana cewa babu mamaki shugaban kasar ya yi jawabi ga al’umman kasar a yau Juma’a bayan dogon hutu da yayi, domin ya kwatar da tarzoma kan karfinsa na mulki.

Mataimakin san a musamman a shafin zumunta, Femi Adesina ne ya saki labarin dawowar nasa a daren jiya a cikin jawabin sa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel