Shugaba Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Ogbemudia

Shugaba Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Ogbemudia

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna juyayinsa game da rahotannin cewa wani tsohon gwamnan Bendel ( tsohuwar jiha) Dr. Samuel Osaigbovo Ogbemudia, ya rasu jiya da dare.

Buhari ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan mariyagi Ogbemudia

Buhari ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan mariyagi Ogbemudia

A wata jawabin da mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayar yace Dr. Samuel Osaigbovo Ogbemudia, yayi kafa tarihin kokari ga jiharsa.

Ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan Ogbemudia da kuma gwamnatin jihar Edo akan rasuwan tsohon gwamnan su.

KU KARANTA: Buhari bai halarci sallan Juma'a ba

Jawabin tace: “ Shugaba Buhari ya nuna juyayin mutuwar wani jigo wanda ya bautawa kasarsa sosai a matsayin soja, da kuma gwamnan demokradiyya.

“Shugabn kasan ya tuna rawan da marigayin taka wajen daow da gwamnatin demokradiyya a 1999 kuma yanada tabbacin cewa ba za’a manta da shi ba bisa abinda yayiwa mutanensa musamman a bangaren ilimi, kula, da cigaba."

Dr. Samuel Osaigbovo Ogbemudia, ya mutu ne misalin karfe 11 na dare ranan Alhamis, 9 ga watan Maris a asibiti.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel