“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – inji Buhari

“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar waje a ranar juma’a 10 ga watan Feburairu bayan kwashe kwanaki 50 ana duba lafiyarsa a kasar Birtaniya.

“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – Buhari

“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – Buhari

Sai dai a cikin jawabin da shugaban yayi a fadar gwamnati, yace akwai bukatar ya sake komawa can kasar Birtaniyan nan bada dadewa ba don a kara duba lafiyarsa.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin dayayi inda yace “Ina matukar godiya ga yan Najeriya, musulmai da Kirista wadanda suka yi min addu’ar samun sauki da fatan alheri. Wannan wata manuniya ce dake nuna cewar duk da halin matsin da ake ciki, yan Najeriya suna baiwa gwamnati goyon baya don cimma burinta.

KU KARANTA: Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – Buhari

“Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – Buhari

“Hanya mafi dacewa da zan bi in gode muku itace in dage wajen yi muku hidima, kare muradunkun tare da rike amanar da kuka bani hannu biyu biyu. Nagode muku sosai.

“Ina samu sauki yanzu ba kamar da ba, amma wata kila in sake komawa don a kara duba ni a cikin yan satuttuka masu zuwa” inji shugaba Buhari.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yace ya gode ma Allah daya dawo da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin koshin lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel