Ana koro ‘Yan Najeriya daga kasar Amurka

Ana koro ‘Yan Najeriya daga kasar Amurka

A Ranar Litinin ne shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannu a wata doka da za ta hana wasu ‘yan kasashen Musulmai shigowa cikin kasar Amurka. A cikin kasashen dai babu Najeriya amma ‘yan kasar na fuskantar barazana

Ana koro ‘Yan Najeriya daga kasar Amurka

Ana koro ‘Yan Najeriya daga kasar Amurka

Ofishin Jakadancin kasar Amurka ta fito tayi bayani game da fatattako ‘Yan Najeriya da ake yi daga kasar Amurka. Jakadancin tace ba mamaki dokar shugaba Trump ne ke aiki har ta ja abin yake kokari ya shafi ‘Yan Najeriya.

A baya dai shugaban kasa Donald Trump yayi wannan yunkuri na hana Musulman wasu kasashe shiga Amurka sai dai babu Najeriya a cikin jerin kasashen. Sai dai kuma gas hi ana samun wasu lokuta da ake koro ‘Yan Najeriya daga kasar.

KU KARANTA: Na ji sauki Inji Shugaban Najeriya

Kwanan nan aka kora wani ‘Dan Najeriya mai suna Femi Olaniyi daga filin jirgin Los Angeles na California kamar yadda muka samu labari daga Jaridar Premium Times. An dai maida wannan mutumi gida duk da cewa yana da takardun biza bayan an garkame sa na kwanaki.

A Najeriya kuma Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban hukumar fasa-kwauri na kasa Kanal Hamid Ali mai ritaya a game da dokar da aka kawo na takardun mota. Sanatocin suka ce dole shugaban kwastam yayi mata bayani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Murnar Buhari ya dawo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel