“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya fuskanci kalubale daban daban a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasa.

“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

Mataimakin shugaban ya bayyana haka ne yayin wata kwarya kwarayar taron tarba na mintuna 30 da aka shirya ma shugaban kasar a sashin uwargidar shugaban kasa dake fadar shugaban gwamnati jim kadan bayan dawowarsa Najeriya daga birnin Landan.

Farfesa Osinbajo ya rike mukamin mukaddashin shugaban kasar Najeriya daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa 9 ga watan Maris.

KU KARANTA: Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Mataimakin shugaban ya gode ma shugaba Buhari daya amince da shi har ya bashin ragamar tafiyar da mulkin Najeriya na tsawon kwanaki 50, kuma yace majalisar zartarwa na matukar godiya da Allah daya dawo da Buhari gida cikin koshin lafiya.

“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

“Na fuskanci ƙalubale bayan tafiyar ka” Osinbajo ya faɗa ma Buhari

Osinbajo yace “Ya shugaban kasa, a madadi na da sauran yayan majalisar zartarwar kasa, ina yi maka maraba da dawowa, muna yi ma Allah godiya daya sa ka dawo mana lafiya. Ya shugaban kasa, yan kwanakin dana kwashe ina jan ragamar mulki sun kayatar dani.

“da farko dai ina so in gode maka da amincewar da kayi da ni da har ka sakar min ragamar mulki a matsayin mukaddashin shugaban kasa. A gani na, abu mafi muhimmanci shine yadda ka gamsu da tsarin mulkin kasar na.

“Tsarin mulkin kasa da muka rantse da shi shine mafi muhimmanci kuma ya tanadar da yadda ya kamata a tafiyar da gwamnati. Ni kam a kayace nake saboda yadda na dinga zagaye kasar nan, duk da cewa hanyoyin basu da kyau. Don haka na fuskanci kalubale da dama. Amma nagode da goyon bayan da shugaban kasa ya bani.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel