Jami’an tsaro sun shiga gidan wani Sanata

Jami’an tsaro sun shiga gidan wani Sanata

Jami’an tsaro na Najeriya sun shiga gidan wani Sanata a Jihar Kaduna a Jiya Ranar Alhamis kamar yadda muka samu labari.

Jami’an tsaro sun shiga gidan wani Sanata

Jami’an tsaro sun shiga gidan wani Sanata

Jami’an tsaro masu fararen kaya watau DSS sun shiga gidan Sanata Danjuma La’ah na Jihar Kaduna a jiya inda suka yi masa daya-daya. Mun samu labara dai cewa Jami’an na DSS sun isa gidan ne a wata katuwar mota inda suka yi ta bincike.

Jami’an tsaron dai wadanda sun fi 100 kamar yadda muka samu labara sun burma gidan Sanata Danjuma La’ah da ke Garin Kaduna inda suka lalata wasu daga cikin kayan gidan irin su tebura da kuma kujeru. Jami’an dai ba su nuna takardar da ta ba su wani izinin bincike ba.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya dawo

Wadanda su ke gidan a lokacin sun bayyana cewa an yi wa masu gadin gidan ba dai-dai ba yayin da suka barntar da dukiya. Jami’an na DSS dai kuma sun yi gaba da wasu ‘yanuwan Samatan mai wakiltar kudancin Kaduna inda har yanzu ba a gan su ba.

Kuma dai Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN ta koka game da yadda ta rasa ‘ya ‘yan ta a rikicin Kudancin Kaduna. Kungiyar tayi kuka inda tace har yanzu ana kashe mata Jama’a a boye. CAN tace duk da cewa akwai Jami’an tsaro a Yankin Kudancin Kaduna ana yi mata kisan dauki dai-daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Murnar dawowar Buhari a Daura

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel