Mazaunan Kano na murnar dawowar shugaba Buhari

Mazaunan Kano na murnar dawowar shugaba Buhari

- Mazaunan Kano na farin ciki da godiya ga Allah bayan labarin dawowar shugaba Buhari.

- Shugaban ya dawo Najeriya a ranar jumma’a, 10 ga watan Maris bayan hutun ganin likita a Landan.

Mazaunan Kano na murnar dawowar shugaba Buhari

Mazaunan Kano na murnar dawowar shugaba Buhari

Mazaunan garin Kano na cike da farin ciki da godiya ga Allah bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar jumma’a, 10 ga watan Maris.

Kamfanin dilancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa, shugaban kasa ya isa filin jirgin sama na sojojin sama na Kaduna a misali karfe 7:40 na safe a ranar Jumma'a bayan hutun ganin likita a kasar Birtaniya.

Wasu daga cikin mazaunar sun shaidawa NAN cewa, sun kasance masu farin cikin dawowar shugaban kasa da kuma ganin cewa ya dawo cikin koshin lafiya.

Wani mazaunin, Mukhtar Dahiru-Rigachikun ya ce: “Ina matukar farin ciki da dawowar shugaban kasa yayin da kuma ya dawo cikin koshin lafiya”.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya umarci Osinbajo ya cigaba rikon kwarya, yana bukatan hutawa kadan

Mukhtar ya bukaci 'yan Najeriya musulmai da kuma kiristoci cewa su cigaba da addu’a don zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Ya ce: "Ko da yake, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yi yi rawan gani a matsayin mukaddashin shugaban kasa bayan tafiyar shugaba Buhar, amma yanzu sa su hada hannu don ci gaban kasar”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel