Aisha Buhari ta nuna godiya ga yan Najeriya yayinda mai gidanta ya dawo

Aisha Buhari ta nuna godiya ga yan Najeriya yayinda mai gidanta ya dawo

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta tarbi mai gidanta, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a tsakanin yan’uwa da abokan arziki, wadanda suka zo don taya ta tarban shugaban kasa daga dogon hutun da ya je.

Aisha Buhari ta nuna godiya ga yan Najeriya yayinda mai gidanta ya dawo

Uwargidan Buhari, wacce ta tarbi shugaban kasar da misalin karfe 9a.m na safe, a gidansu dake fadar shugaban kasa, Abuja, tayi godiya ga yan Najeriya kan goyon baya da addu’an su ga shugaban kasar.

Wadanda suka taya uwargidan shugaban kasar tarban mai gidan nata sun hada da Misis Dolapo Osinbajo, uwargidan mataimakin shugaban kasa, matayen gwamnoni, ministoci, yan’uwa da makusantan ta.

KU KARANTA KUMA: Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Uwargidan Buhari, wacce ke cikin farin cikin dawowar mijin ta, ta nuna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya dawo da shugaban kasar lafiya.

A wani labara makamancin wannan, shugaban ma’aikatan tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita, ta nuna jin dadinda ga dawowar shugaban kasar.

Oyo-Ita ta bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yiwa shugabannin su addu’a domin su samu damar shugabantar mutane da kyau.

Har ila yau da take magana, mataimakiya na musamman ga uwargida shugaban kasa Dr Hajo Sani, ta nuna farin cikin ta ga dawowar shugaban kasa kasar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel