Fashola ya maidawa Ambode martani

Fashola ya maidawa Ambode martani

– Gwamnan Jihar Legas ya zargi Minista Fashola da kawo masa cikas wajen wasu ayyuka

– Ministan ayyukan ya maidawa Gwamna Ambode martani

– Fashola ya wanke kan sa daga zargin Magajin na sa

Fashola ya maidawa Ambode martani

Fashola ya maidawa Gwamna Ambode martani

Da alamu ana samun rikici tsakanin Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode da tsohon Gwamnan wanda yake Ministan tarayya a yanzu watau Babatunde Raji Fashola. Ambode ya zargi Minista Fashola da kawo masa tasgaro wajen gudanar da wasu ayyuka.

Ministan tarayyar Raji Fashola yace ko kadan Gwamnatin tarayya ta ma’aikatar sa ba tayi hakan ba. Gwamna Ambode yace ma’aikatar ayyuka ta hana sa gina wani titi da ya lalace a Jihar. Fashola yace ya kira Gwamnan domin yayi masa bayanin yadda abubuwan suke.

KU KARANTA: Sanatoci sun gayyaci Hamid Ali

Fashola ya maidawa Ambode martani

Minista Fashola ya maidawa Ambode martani

Wani titi ne dai a kan hanyar babban filin jirgin sama na Jihar wanda Gwamnan yace yana bukatar gyara. Ministan yace Gwamnatin tarayya tayi wa Legas ayyuka da dama wanda har yanzu akwai wasu hanyoyi 3 da ake shirin gyarawa na Jihar don haka maganar Gwamnan ba gaskiya bace.

A Jihar Benuwe ma dai Gwamna Ortom ya kuma yi kaca-kaca da tsohon Gwamna Gabriel Suswam yace bai tsinana komai ba a lokacin da ya mulki Jihar. Gwamna Ortom yana ta fama da kalubale wurin shugabancin Jihar inda yace bai ga aikin da tsohon Gwamnan yayi ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel