Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

A jiya ne muka samu labarin cewa shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari zai dawo gida Yau Jumu’a. A yau da asuba Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo kasar.

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa da ke Aso Villa. Shugaban kasar ya iso filin jirgin sama na Kaduna a Jirgin shugaban kasa, daga nan ya zarce zuwa Birnin Tarayya, dazu haka shugaban ya shiga Fadar Aso Villa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da iyalin sa; Shugaban kasar ya hadu da Mai dakin sa Hajiya Aisha Buhari da kuma Uwargidar Mataimakin shugaban kasa Misis Dolapo Osinbajo da wasu Jikokin sa.

KU KARANTA: Hotuna da Bidiyon dawowar Buhari

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa

Majiyar mu ta nuna mana cewa an yi wani dan karamin biki domin shigowar shugaban kasar. Mun samu rahoton cewa shugaban kasar ya gana da Ministocin sa a Fadar wanda daga ciki akwai Rotimi Amaechi.

Har wa yau dai mun ji labarin cewa shugaban kasar yace jikin say a murmure, shugaban kasar yace yanzu yana jin kan sa wasai. Tun a inda ya sauka wani Dan Jarida ya tambaye sa ko ya jikin sa, shugaba Buhari ya fada masa cewa ai ga shi nan yana ganin sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel