Yadda shugaban kasa ya dawo

Yadda shugaban kasa ya dawo

A jiya ne muka samu labarin cewa shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari zai dawo gida Yau Jumu’a. Shugaba Muhammadu Buhari dai ya dauki kusan kwanaki 50 a Landan

Yadda shugaban kasa ya dawo

Yadda shugaban kasa ya dawo

A yau ne shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya da asuba. Shugaban kasar ya iso filin jirgin sama na Kaduna a Jirgin shugaban kasa na Air force kimanin karfe 4:00 na safiya. Mataimakin Gwamnan Jihar Bala Bentex suka tarbe sa.

Bayan nan ne shugaban kasan ya karasa Birnin Tarayya Abuja a wani dan karamin jirgi, A nan dai Mukaddashin shugaban kasa da sauran kusoshin Gwamnati sun dade suna jiran sa. An ga Farfesa Osinbajo da mai ba shugaban kasa shawara game da harkar tsaro Manjo-Janar Munguno suna ta tattaunawa.

KU KARANTA: Dubi yadda Buhari ya dawo

Yadda shugaban kasa ya dawo

Shugaba Buhari ya dawo

Bayan lokaci kadan sai ga jirgin shugaban kasar nan ya dura, Jami’ai kuma suka zagaye sa ya fito. Shugaba Buhari ya fara gaisawa da Mataimakin sa Farfesa Osinnajo sannan ya gaisa da Abba Kyari da kuma Gwamnan Zamfara da Ministan Abuja, sannan ya gaisa da sauran manyan Jami’ai.

Shugaba Buhari ya gaisa da Femi Adesina kenan sai wani Dan Jarida ya tambaye sa ko ya jikin sa. Shugaba Buhari ya fada masa cewa ai ga shi nan yana ganin sa. Nan shugaban kasar ya shiga motar sa ta Marsandi S550 zuwa Fadar Aso Rock.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel