Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya da misalin karfe 4.am na ranar Juma’a, 10 ga watan Maris bayan dogon hutu da yayi a birnin Landan.

A cewar jaridar Thisday, sakamakon rufe filin jirgin saman Abuja an shirya saukar jirgin sa a filin jirgin Kaduna a safiyar ranar Juma’a, bayan shawarar da aka yanke na dawo dashi a jirgi mai saukar ungulu zuwa fadar shugaban kasa, Abuja.

Ana ta sanya ran dawowar shugabna kasar a karshen wata amma ya aiko da wani wasika ga majalisar dokoki inda ya sanar da su shawarar da ya yanke da kara hutunsa kan dalilin lafiyar sa.

Dogon hutun nasa ya kawo rudani game da lafiyar sa tare da jita-jita da ake ta yadawa kan cewa ya mutu duk da cewan mataimakan sa a kafofin yada labarai, Garba Shehu da Femi Adesina suna karyata hakan lokuta da dama.

Har ila yau ana ta kawo rudani kan cewa shugaban kasar na iya kaiwa watanni hudu a birnin Landan saboda lafiyarsa ko da dai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya jagoranci tawagar mutane uku da suka hada da shi kansa, kakakin majalisa Yakubu Dogara da kuma Ahmed Lawani domin haduwa da Buhari a Landan.

Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Bayan ganawar da shugaban kasa Saraki ya nace kan cewa yana cikin koshin lafiya.

Bayan tawagar da Saraki ya jagoranta, shugaban kasar ya karbi bakoncin manyan mutane a gidan Abuja dake Landan wanda suka hada da shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu da Cif Bisi Akande.

Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Uwargidansa ma Aisha ta kai masa ziyara don tabbatar way an Najeriya cewa yana cikin koshin lafiya haka kuma gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun.

Bakon karshe da ya tarba kafin dawowarsa Najeriya shine Rt Hon Justin Welby, babban fasto na duniya wanda ya kai masa ziyara a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris.

Kalli jirgin da ya dawo da Buhari Najeriya

Kalli bidiyon dawowar Buhari:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel