Daga karshe shugaban kasa Buhari ya dawo Najeriya, ya iso da karfe 4 a.m

Daga karshe shugaban kasa Buhari ya dawo Najeriya, ya iso da karfe 4 a.m

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a da misalin karfe 4 a.m, bayan kwanaki 51 da barin kasar don hutun ganin likita.

Daga karshe shugaban kasa Buhari ya dawo Najeriya, ya iso da karfe 4 a.m

A cewar jaridar Thisday, sakamakon rufe filin jirgin saman Abuja an shirya saukar jirgin sa a filin jirgin Kaduna a safiyar ranar Juma’a, bayan shawarar da aka yanke na dawo dashi a jirgi mai saukar ungulu zuwa fadar shugaban kasa, Abuja.

Majiyar ta kuma bayyana cewa babu mamaki shugaban kasar ya yi jawabi ga al’umman kasar a yau Juma’a bayan dogon hutu da yayi, domin ya kwatar da tarzoma kan karfinsa na mulki.

Mataimakin san a musamman a shafin zumunta, Femi Adesina ne ya saki labarin dawowar nasa a daren jiya a cikin jawabin sa.

Da yake tabbatar da al’amarin, gwamnan jihar Kaduna, El Rufai ya rubuta a shafin san a Facebook:

“SANNU DA DAWOWA PMB: Shugaban kasa ya dawo. Ya sauka Kaduna Lafiya sannan kuma Mukaddashin Gwamna Barnabas Yusuf Bala da manyan jami’an KDSG sun tarbe shi. Gwamnati da mutanen jihar Kaduna na alfaharin tarban shugaban kasar da ya dawo gidan sa don ya fuskanci ayyukan sake gina Najeriya. Alhamdulillah. Jumaat Mubarak ga kowa,” inji shi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel