Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

A game da tattalin arziki an yi kira ga Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi koyi da irin tsarin tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck

Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

Wani mai ba tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan Goodluck shawara yayi kira ga Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi koyi da irin tsarin tsohon shugaba Jonathan Goodluck na yarjeniyar man fetur.

Dr. Doyin Okupe yace ya kamata Gwamnati ta shiga yarjejeniyar musayar man fetur maimakon ta rika bata Dala a banza. Najeriya dai tana kashe makudan dalolin kudi wajen shigo da tataccen man fetur cikin kasar.

KU KARANTA: An sa ranar zaben shugaban kasa

Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

Na kusa da Jonathan sun ba Gwamnatin Buhari shawara

Bisa wannan dalili ne Gwamnatin Jonathan ta shiga irin wannan tsari domin samun saukin kashe dalolin Amurkar da kasar ta ke da su. Yanzu haka dai Bankin CBN ne ke ba ‘yan kasuwa tsurar dala domin su shigo da man fetur. Dr. Okupe yace idan aka rika musanya, Dalar ta huta.

Haka kuma kason da Najeriya ta ke samu daga gas ta hannun NLNG yayi kasan da ba a taba jin labarin irin sa ba cikin shekaru 10. Najeriya dai ta samu sama da Dala Biliyan $1 a 2015 a matsayin kason ta na gas sai dai wannan shekarar da ta wuce abin da aka samu Dala Miliyan 365 ne kacal.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel