Hukumar INEC ta alanta ranan zaben 2019

Hukumar INEC ta alanta ranan zaben 2019

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta alanta ranan 16 ga watan Fabrairu a matsayin ranan da za’a gudanar da zaben shugaban kasan 2019.

YANZU-YANZU: Hukumar INEC ta alanta ranan zaben 2019

YANZU-YANZU: Hukumar INEC ta alanta ranan zaben 2019

Kwamishanan INEC na yankin kudu maso yamma, Solomon Soyebi, ya bayar da wannan sanarwan ne a wata hira a yau Alhamis, 9 ga watan Maris a Abuja.

Kana kuma Soyobi ya bayyana cewa hukumar zata gudanar zaben gwamnoni- majalisar dokokin jiha da a Abuja a ranan Asabar, 2 ga watan 2019.

KU KARANTA: Sarkin musulmi yayi magana mai tsauri ga Osinbajo

Wani sashen jawabin yace: “ A Najeriya, kundin tattalin arzikin Najeriya ta bada tsarin cewa a gudanar da zabe akalla saura kwanaki 30 kafin karewar wa’addin gwamnatinsa. Domin tabbatar da kwanankin zabe da kuma shiri na kwarai ga hukumar, jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, masu takara, da masu ruwa da tsaki, hukumar ta yanke shawaran sanya ranan gudanar da zabe a mako na 3 a watan Fabrairu, sannan na gwamnoni mako biyu nag aba. Sabod haka, za’a gudanar da zaben shugaban kasa da majalisan dokokin tarayya ranan asabar, 16 ga watan Fabrairu 2019, sannan a gudanar da na gwamnoni, majalisun dokokin jiha, da birnin tarayya ranan asabar, 2 ga watan Maris, 2019.

Jama’a, zaku tuna cewa a makon da ya gabata, mun sanar da ku cewa zamu yanke shawara wannan mako bisa ga rahoton kwamitin ladabtarwa tayi akan ma’aikatan INEC da hukumar EFCC take tuhuma akan magudin zaben 2015.”

A bangare guda, an nemi hukumar INEC tayi dubi cikin dokar INEC kafin a gudanar da zaben 2019. Wata gangamin jam’iyyun siyasa 25 ne sukayi wannan bukata a ranan Laraba, 8 ga watan Maris.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel