Rikicin Kudancin Kaduna: Har yanzu akwai sauran kura

Rikicin Kudancin Kaduna: Har yanzu akwai sauran kura

Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN ta koka game da yadda ta rasa ‘ya ‘yan ta a rikicin Kudancin Kaduna. An dai rasa rayuka masu dinbin yawa a rikicin da ake fama da shi

Rikicin Kudancin Kaduna: CAN ta koka

Rikicin Kudancin Kaduna: Har yanzu akwai sauran kura

Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN tayi kuka inda tace har yanzu ana kashe mata Jama’a a boye. CAN tace duk da cewa akwai Jami’an tsaro a Yankin Kudancin Kaduna ana yi mata kisan dauki dai-daya.

CAN din tace har yanzu fa Jama’an ta ba su tsira ba hakan ta sa wani babban Rabaren na coci ya kira Sufetan ‘Yan Sanda ya shawo kan lamarin. An dai bayyana cewa kwanan nan aka kashe wani yayin da yake aiki a gonar sa.

KU KARANTA: Ana rikici tsakani Gwamna da magajin sa

Rikicin Kudancin Kaduna: Har yanzu akwai sauran kura

Rikicin Kudancin Kaduna: Har yanzu akwai sauran kura

Rabaren Pam ya kuma kira Gwamnan Jihar ya tuntubi sauran Gwamnoni game da yadda za a kawo karshen rikicin yankin musamman tsohon Gwamna Ahmed Muhammad Makarfi. Rabaren din dai ya yabawa kokarin mukaddashin shugaban kasa Osinbajo game da rikicin.

Wata Kungiya kuma mai suna CDD tayi tir da shugaban kasa Muhammadu Buhari inda tace yayi wa ‘Yan Najeriya alkawura da dama a lokacin yakin neman zabe kuma ya gaza cikawa face guda daya rak.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel