Gwamnan Benuwe yayi kaca-kaca magajin sa

Gwamnan Benuwe yayi kaca-kaca magajin sa

– Gwamna Ortom ya bayyana cewa tun ba yau ba ya san cewa zai zama Gwamna

– Samuel Ortom yace tun shekaru 25 da suka gabata ya san cewa zai riki wannan Jiha

– Gwamnan yace Ubangiji ne dai ya nuna masu haka

Gwamnan Benuwe yayi kaca-kaca magajin sa

Gwamnan Benuwe yayi kaca-kaca magajin sa Suswam

Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa tun ba yau ba ya san cewa zai zama Gwamnan Jihar Benuwe. Gwamnan yace tun shekaru 25 da suka wuce Ubangiji ya nuna masa cewa zai mulki Jihar ta sa.

Gwamna Ortom yace hawan sa kujerar wani abu ne kurum na ikon Allah. Gwamnan dai yace an umarce sa ya zama mai gaskiya da kuma adalci wajen sha’anin mulki. Gwamna Ortom ya kuma yi kaca-kaca da tsohon Gwamna Gabriel Suswam yace bai tsinana komai ba.

KU KARANTA: Makarantar da ake karatu a kasa

Samuel Ortom dai yace tun a shekarar 1992 aka nuna masa cewa zai mulki Jihar ta Benue don haka ya shiga shiri tuni. Tsohon Ministan dai yana ta fama da kalubale wurin shugabancin Jihar inda yace duk laifin tsohon Gwamnan ne.

Kwanaki can abban Limamin Cocin Grace and Light Pentecostal da ke Garin Makurdi a Jihar Benue yace Gwamnan Jihar, Samuel Ortom ba zai cigaba da zama a kujerar sa ba bayan shekarar 2019 don kuwa shi ya leka ya gano. Limamin yace an umarce sa daga sama ya sanar da Gwamnan cewa ba zai yi tazarce ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel