Almajiri ya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi, amma ko kasan dalilinsa na mayarwa?

Almajiri ya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi, amma ko kasan dalilinsa na mayarwa?

Wani mutumin kasar Kenya ya zubar da kudi KSh 200,000, kwatankwacin N615,000 yayin dayake kokarin tsallaka titi akan hanyarsa ta zuwa banki don ajiye kudin a asusunsa.

Almajiri ya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi, amma ko kasan dalilinsa na mayarwa?

Almajiri a kasar Kenya

Sai dai yayin dayake cikin tafiya ba tare da lura ya zubar da kudaden ba, sai yaji wani matashi yana kiransa, koda ya juya, sai ya ga wani almajiri ne ke kiransa, a tunaninsa zato yake zai roke shi kudi ne, don haka sai yayi watsi da shi ya shige cikin banki.

KU KARANTA: Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000

Almajiri ya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi, amma ko kasan dalilinsa na mayarwa?

Almajirin daya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi

Shi kuwa almajirin ya cigaba da binsa har gaban kofar bankin, inda ya tare shi, nan ne fa mutumin ya tsaya don ya saurare almajirin.

Sai almajirin yace masa, "Uliangusha pesa huko nyuma” ma’ana, “ka zubar da kudinka yayin dake kokarin tsallaka titi,” kumaya mika masa kudin nasa ya juya ya wuce.

Almajirin ya kara da cewa ya dawo mai da kudin ne saboda yana tunanin wata kila zai biya kudin asibiti ne ko kudin makarantar, inda ya shawarce shi da yayi maza ya shigar da kudin cikin asusunsa kafin ya kara zubar dasu.

Haka kuwa aka yi, mutumin ya shige banki, amma koda ya fito tuni yaron ya bace, ya kama gabansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel