Tsoro a jihar Niger yayinda wasu matsafa suka kai farmaki makarantar islamiyya sannan suka yanka yara 3

Tsoro a jihar Niger yayinda wasu matsafa suka kai farmaki makarantar islamiyya sannan suka yanka yara 3

Wani mummunan kungiyar matsafa sun sanya mutane dama cikin alhini matuka bayan sun mamaye wani makarantar Islamiyya sannan kuma suka yanka yara.

Wasu matsafa dake bukatar jinni sun kashe wasu yara maza guda uku da misalign karfe uku na daren ranar Laraba a wani makarantar Islamiyya dake Tungan Magajiya, karamar hukumar Rijau dake jihar Niger.

Tsoro a jihar Niger yayinda wasu matsafa suka kai farmaki makarantar islamiyya sannan suka yanka yara 3

Da farko matsafan sun kai hari ga yara biyar ne. Biyu cikin yaran sun mutu a take yayinda dayan da akayi gaggawan kaiwa asibiti yam utu daga baya. An cire makogoron yaran sannan aka dibi jininsu a wani roba don amfani da shi, yaran da aka kashe suna tsakanin shekaru takwas da 13 a duniya.

A cewar jaridar Vanguard, daya daga cikin malamin da abun ya shafa ya tabbatar da cewa an kai hari ga yaran ne yayinda suke bacci sannan kuma aka cire masu makogwaro.

KU KARANTA KUMA: Fada ya barke yayinda wani mutumi ya sanya wa Karen sa suna Muhammad a Kaduna

Jami’in kula da huldan jama’a na hukumar yan sandan jihar Niger, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da al’amarin, inda yace an kai harin ne a kan maza biyar amma uku sun mutu.

Elkana ya ce: “anyi zargin cewa matsafa ne saboda sun dibi jinin yaran ne da misalign karfe 3 na safe a ranar Laraba.”

Ya bayyana cewa ana nan ana gudanar da bincike kuma cewa za’a bi sahun wadanda suka aikata laifin yayinda yace biyu daga cikin yaran sun rayu sannan yaba da tabbacin cewa za’a gurfanar da masu laifin a gaban shari’a da zaran an cefke su.

Abun bakin ciki!

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel