DSS ta kashewa wani Limami ido bayan ya ci jibga

DSS ta kashewa wani Limami ido bayan ya ci jibga

Hukumar DSS ta kasa ta kusa kashe wani Fasto a Legas da mugun duka. An dai kama Faston ne a kan wani laifi da yaron sa ya aikata, nan aka shiga dukan sa kamar Ubangiji ya aiko su.

DSS ta kashewa wani Limami ido bayan ya ci jibga

DSS ta kashewa wani Limami ido bayan ya ci jibga

Majiyar mu ta bayyana mana cewa an damke wani Limamin babban cocin Gracious and Mercy Prophetic International da ke Garin Legas. Yanzu haka wannan Fasto har ya rasa idanun sa a dalilin dan-karen dukan da ya sha a hannun Jami’an tsaro.

Wani yaro ne dai da ke aiki a gidan Faston ya aikata laifi, hakan ta sa aka iske Faston har gida aka damke sa da ba a samu wannan yaro ba. Wannan yaron ya damfari Jama’a da dama ta hanyar yi masu musayar kudin dalar Amurka na kudin jabu.

KU KARANTA: An cafke Sojin karya a Jihar Ribas

An dai zo gidan Faston ne da niyyar kama wannan yaro, ko da aka samu ya tsere sai aka kama Faston aka yi gaba da shi cikin mota inda aka yi tayi masu mugun bugu.Yanzu haka dai an ce wannan Limami ya makance bayan da ya ci dukan tsiyar har jinin sa ya sauka.

Haka kuma asirin wani sanannen Fasto ya tonu bayan da aka samu labarin cewa ya yaudari wata Budurwa da yi mata karyar zai aure ta. Wannan Faston yayi ma Budurwar ciki inda ya nemi ya kyale ta nan fat ace fau-fau yayi karya ba za ta yard aba, sai ta sheka kotu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel