Gagaruman abubuwa hudu da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Gagaruman abubuwa hudu da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Yan Najeriya na cikin tsananin son sanin lokacin da shugaban kasar su zai dawo daga dogon hutun da ya tafi, dage-dagen lokacin dawowar yayi yawa.

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Wani rahoto daga Sahara Reporters ya nuna cewa an dakatar da dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Najeriya a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Maris.

A cewar rahoton, likitocin shugaban kasar na ganin cewa baiyi isashen karfin da zai dawo gida ba duk da matsin lambar da na kewaye da shi sukayi.

Niyan su shine su dawo da shi Abuja kafin a rufe filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport a ranar Laraba, 9 ga watan Maris.

Koda dai babu wani kwakwaran hujja, amma har yanzu akwai ikirarin cewa shugaban kasar wanda Ibrahim Dasuki Nakande, wani tsohon ministan bayanai na jiha, yayi ikiracin cewa zai dawo Najeriya a ranar 6 ga watan Maris, zai dawo a wannan watan na Maris.

Ga abubuwa 4 da ake sa rai idan ya dawo:

1. Osinbajo zai daina aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasa

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Kamar yadda ake sa rai, mukaddashin shugaban kasar Najeriya mai nasara, Farfesa Yemi Osinbajo zai koma matsayinsa na mataimakin shugabna kasa, yunkurin da zai sa wasu cikin bakin ciki, tunda cewa yana ta aiki sosai.

APC will lash out at detractors

2. Jam’iyyar APC zata maida martani ga yan hana ruwa gudu

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Ana ta daura dukkan laifuka da zarge-zarge game da rashin shugabna kasa a kasar kan Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Don haka babu shakka jam’iyyar mai ci zata mayar da martani ga dukka wadanda ke ta yayata maganganu a kan shugaban kasa da gwamnatin sa yayinda yayi tafiya.

3. Masu yada jita-jita zasu nemi sabon tatsuniyar da zasu rike

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Akwai mutane da dama dake ta ci daga yada jita-jita game da halin da lafiyar shugaban kasar ke ciki da kuma yadda yan kasa ke ta ji kan rashin sa a kasa.

Idan shugaban kasar ya dawo cikin koshin lafiya, za’a dunga yiwa ruwayoyinsu kallon shirme, amma babu shakka bazasu tsaya a nan ba, zasu nemi sabon hanyan fuskanta.

4. Shugaban kasar zai ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

Gagaruman abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya dawo a watan nan na Maris

A matsayinsa na mutun mai tsayawa da jajircewa a kan maganar sa, babu shakka da zaran shugaban kasa Buhari ya dawo zai sanya wa motar yaki da cin hanci da rashawarsa mai.

A bayan sa hukumomin yaki da ci hanci da rashawa na ta ci gaba da aiki, amma babu shakka idan ya dawo za’a kara kaimi gurin gurfanar da yan Najeriya masu cin hanci da rashawa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel