2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

A wani nazari da Jaridar Daily Trust tayi mun kawo maku jerin ‘yan siyasan da ke iya tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa na 2019. Mun kawo ‘yan siyasa da dama, a wannan karo za mu karasa jerin.

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

Ali Modu Sheriff

Kamar dai Ahmed Makarfi, ana ta rikicin kujerar PDP da Ali Sheriff. Tsohon Gwamnan na Jihar Borno ba bakon siyasa bane don kuwa kafin nan yayi Sanata ba sau daya ba. Sheriff babban dan siyasa ne kuma ba shakka yana harin tikitin PDP a zabe mai zuwa.

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

Ayo Fayose

Wasu na masa kallon gwarzo jarumi yayin da wasu kuma ke masa kallon mashirmaci kurum. Amma ba shakka Ayo Fayose na da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa don kuwa ya fadi hakan da kan sa.

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

KU KARANTA: Osinbajo na iya rufe gurbin Buhari-Inji matar shugaban kasa

Rochas Okorocha

Okorocha yayi takarar Gwamna da ma shugaban kasa bai samu ba tun a baya kafin ya samu sa’a ya zama Gwamnan Jihar Imo. Ko da aka kafa APC Okorocha yana cikin ‘yan sahun farko ya kuma nemi takarar shugaban kasa yayin da Muhammadu Buhari ya kada sa karbar tuta. Okorocha dai ana masa kallon Dan Najeriya ne ba Inyamuri ba.

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

Sauran ‘yan takara

Akwai wasu da mamaki su ke harin kujerar Buhari irin su tsohon Gwamnan Legas Babatude Fashola wanda yake Minista a yanzu da kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani wanda ya koma APC kwanan nan, watakila yana harin kujerar ne daga yankin sa na Kasar Ibo. Dsr.

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

2019: ‘Yan siyasan da ke iya kawowa Buhari cikas

[Mun kawo kusan jeri har 3 a baya kafin wannan]

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel