Yan bindiga sun buɗe wuta a gidan Olisa Metuh dake Abuja

Yan bindiga sun buɗe wuta a gidan Olisa Metuh dake Abuja

Wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne sun kai farmaki gidan tsohon kaakakin jam’iyyar PDP Cif Olisa Metuh dake rukunin gidaje na Prince and Princess dake Abuja.

Yan bindiga sun buɗe wuta a gidan Olisa Metuh dake Abuja

Yan bindiga sun buɗe wuta a gidan Olisa Metuh dake Abuja

Kaakakin Olisa Metuh, Richard Ihediwa ne ya bayyana ma NAIJ.com inda yace yan bindigan da yawansu ya kai mutane 8 sun bude wuta ne a gidan, inda suka kutsa kai cikin gidan da karfi da yaji.

KU KARANTA: Rikcin ƙabilanci: Hausawa da Yarbawa sun gwabza a jihar Osun, mutane 5 sun mutu

“Sun ɗaɗɗaure masu gadin gidan tare da direban gidan da igiya a farfajiyar gidan, inda suka yi kokarin shiga asalin cikin gidan, amma hakan bai yiwun musu ba sakamakon na’ura mai kwakwalwa dake jikin kofofin cikin gidan.

“Da suka gagara shiga cikin gidan ne sai suka yi ma masu gadin dan banzan duka, inda suka umarce su dasu kira musu Olisa Metuh a waya, amma masi gadin suka doge kan cewa lallai Olisa Metuh baya gida, yayi tafiya kudancin kasar nan.” inji sanarwar

Cikin fusata da rashin samund aman shiga cikin gidan, sai yan bindigan suka shiga dakunan dake gefe, ciki har da ofishin Olisa Metuh, inda suka kwashi wasu muhimman takardu da kayayyakin wuta.

“An ga jini a hanyar tafiyarsu, sakamakon ciwo da wani daga cikinsu yaji lokacin da yake kokarin hauro katangar karfe dake zagaye da gidan. Sai dai tuni Olisa Metuh ya mika korafi ga hukumar yansanda don gano wadanda suka aikata masa wannan danyen aiki.

“A yanzu haka masu gadin gidan da direban gidan suna taimaka ma hukumar yansanda a binciken da suke yi.” Kamar yadda sanarwa ta shaida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel