Biafra: ‘Ɓallewa daga Najeriya ba zai magance matsalolin ku ba’ inji Fasto Charles

Biafra: ‘Ɓallewa daga Najeriya ba zai magance matsalolin ku ba’ inji Fasto Charles

Babba Faston katolika na yankin Jalingo Bishop Charles Harmawa ya nanata cewar ballewar Biafara daga Najeriya ba shine zai magance matsalolin inyamurai ba.

Biafra: ‘Ɓallewa daga Najeriya ba zai magance matsalolin ku ba’ inji Fasto Charles

Biafra: ‘Ɓallewa daga Najeriya ba zai magance matsalolin ku ba’ inji Fasto Charles

Kamar yadda Faston yake fada, yace babu tabbas na cewa koda an raba kasar, ba za’a sake samun zargin cutar da wani bangare daga cikinsu ya sake tasowa ba.

Kungiyoyi dake karajin samar da kasar Biafara wato IPOB da MASSOB sun dade suna fafutukan ganin Najeriya ta kyale yankin Inyamurai sun balle sun kafa kasarsu kamar yadda aka yi a kasar Sudan, kungiyoyin sun ce basu gamsu da kasancewarsu a Najeriya ba, inda suka bayyana Najeriya a matsyain gandun dabbobi.

A wata hira da yayi, Fasto Charles yace kamata yayi shuwagabannin Najeriya su samar d hanyoyin magance zarge zargen rashin adalci da nuna bambamci da wasu kabilu suke ikirarin ana musu.

KU KARANTA: Sojoji sun kama wani sojan gona sanye da khaki sama da kasa

Harmawa yace: “Da fari ina so in tabbatar da cewa mutane nada daman zaben zama abinda ya kwanta musu, amma akwai hanyoyin da suka kamata a bi wajen cimma wannan dama.

“Amma ban yarda da batun cewa wai yan Najeriya bakin juna ne ba, wannan zancen banza ne, don kuwa ba’a kan Najeriya farau ba. Akwai kasashe dayawa a duniya wadanda suke da kabilu da dama fiye da Najeriya. Idan ba haka ba me yasa muke hankoron kulla alaka da sauran kasashen duniya alhalin ba yaren mu ko al’adan mu daya dasu ba?

“Ina sane da irin rashin adalcin da ake yi ma al’umman kasar nan, kuma ina mai ra’ayin ya kamata gwamnati tayi maganin hakan, amma bana tunanin ballewa ne maganin matsalar. Musamman yadda babu tabbacin idan an balle za’a samun adalcin da ake bukata.

“Kamar yadda ake samun almundahanar kudade a gwamnatin tarayya, haka ake samu a gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomin.”

Dayake bayani kan hanyoyin shawo kan matsalar, Fasto Hamarwa yace “Kamata yayi mu fi nuna damuwa da yadda za’a magance matsalolin rashin adalci dana nuna bambamce bambamce da suka addabi kasar, tare da rashin adalci wajen rabon kudaden gwamnati da sauran su.

“Sai kuma muyi tunanin yadda zamu zauna da juna cikin zaman lafiy a matsayin kasa daya al’umma daya, ko muna so ko bama so, kasar mu daya, kuma akwai hikimar hada mu da Allah yayi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel