Abun rabo ne! Barcelona za ta iya cin PSG 6 — Enrique

Abun rabo ne! Barcelona za ta iya cin PSG 6 — Enrique

- Luis Enrique ya ce yana da kwarin guiwa Barcelona za ta iya cin kwallo 6 ta kafa tarihi a gasar Kofin Zakarun Turai, ta yi galaba a kan PSG wadda ta ci ta 4-0, a wasansu na farko

- Sati biyu da ya wuce Barca ta sha kashi 4-0 a gidan Paris St-Germain a wasan nasu na zagayen kungiyoyi 16 karon farko, wanda a yanzu suke son ganin sun yi abin da ba wata kungiya da ta taba yi

Abun rabo ne! Barcelona za ta iya cin PSG 6 — Enrique

Abun rabo ne! Barcelona za ta iya cin PSG 6 — Enrique

Enrique ya ce a cikin minti 95 abubuwa masu yawa za su iya faruwa, saboda haka ya yi amanna za su kasance dab da tsallakewa.

Ya kara da cewa ba wai yana cewa za su tsallake ba ne, amma za su kasance kusa, kuma idan Psg za ta ci su 4, su ma za su iya cinsu 6.

Zakarun na Spaniya sun ci kwallo 11 a wasansu biyu na karshen nan, kuma kwallo daya kawai aka zura musu a raga.

Shi kuwa Luis Suarez cewa ya yi, suna sane da irin mawuyacin halin da suke ciki, to amma a wasan kwallon kafa ba abin da ba zai iya faruwa ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel