Za mu ci gaba da zuba daloli har sa darajar Naira ta dawo - CBN

Za mu ci gaba da zuba daloli har sa darajar Naira ta dawo - CBN

- Babban Bankin Najeriya yace zai ci gaba da samar da daloli cikin kasuwar hada hadar kudade har sai darajar Naira ta dawo

- Yan haka dai babban Bankin Najeriya yana ci gaba da fitar da miliyoyin Daloli zuwa kasuwar hada-hadar kudade, inda a wannan makon ya sako Dala miliyan 367 don cimma bukatun ‘yan kasar

Za mu ci gaba da zuba daloli har sa darajar Naira ta dawo - CBN

Za mu ci gaba da zuba daloli har sa darajar Naira ta dawo - CBN

A makon da ya gabata ma sai da babban Bankin ya sako Dala miliyan 180 ranar Litinin da kuma karin wasu miliyoyi har 350 a ranar Juma’a, don baiwa Naira damar samun daraja a fadin kasar.

Daraktan hulda da jama’a na babban bankin Najeriya, Dakta Isaac Okorafo, yace a duk lokacin da suka saki daloli masu yawa Naira na ‘kara samun daraja.

KU KARANTA: Sanatoci sun dakatar da hukumar kwastam

A cewar Dakta Isaac, akwai masu son shigo da kayayyakin ababen sarrafa masana’antu da kuma na’urori da wadanda kuma ke bukatar canjin domin biyan kudaden makaranta ko zuwa jinya asibiti ko kuma guzuri na asibiti.

Wandanda ke son shigar da kayayyaki na masana’antu sune aka baiwa sune aka baiwa Dala miliyan 367 yayin da wadanda ke son zuwa jinya ko makaranta aka basu Dala miliyan 50.

An dai bukaci Bankunan Najeriya da su rika tabbatar da ganin sun canzawa mutane kudaden, duk wani ‘dan Najeriyar da ya nemi canjin bai samu ba a cikin awa 24 to ya kai ‘karar Bankin zuwa babban Bankin Najeriya domin a dauki mataki akai, inji daraktan hulda da jama’a na babban Bankin Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel