Yadda Dasuki ya biya abokanansa naira biliyan 5.6 don siyo motocin yaki 22

Yadda Dasuki ya biya abokanansa naira biliyan 5.6 don siyo motocin yaki 22

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta bayyana wani shaidanta gaban kotu wanda ya shaida ma kotu cewa tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Sambo Dasuki ya baiwa wasu abokanansa naira biliyan biyar da miliyan dari shidda (N5.6bn) don aikin siyo motocin yaki guda 22.

Yadda Dasuki ya biya abokanansa naira biliyan 5.6 don siyo motocin yaki 22

Yadda Dasuki ya biya abokanansa naira biliyan 5.6 don siyo motocin yaki 22

Shaidan EFCC mai suna Hassan Saidu, wanda jami’in EFCC ne ya bayyana haka ne yayin suararon karar tuhumar da hukumar keyi ma tsohon hadimin Sambo Dasuki Kanal Nicholas Ashinze, da wasu mutane guda uku Wolfgang Reinl, manajan kamfanin Geonel Integrated Services Ltd, sai Barrister Edidiong Ediong da Sagir Mohammed.

KU KARANTA: Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Sauran kamfanunuwa da ake kara sun hada da Unity Continental Nigeria Ltd, Helpline Organisation, Vibrant Resources Ltd da Sologic Integrated Services Ltd. EFCC ta bayyana ma kotu cewa a yanzu haka, kanin Sambo Dasuki Abubakar Ibrahim Dasuki, Kanal Bello Fadile mai ritaya da wani Bello Abayomi sun cika wandunansu da iska.

Saidu ya bayyana ma kotun cewa Dasuki ya aika da kudaden ne daga asusun ofishinsa dake babban bankin Najeriya zuwa ga kamfanunuwan guda 5 ta asusun bankinsu dake Bankin Heritage. Saidu yace an fara biyan su Naira biliyan 3 da miliyan dari da ashirin da biyar (N3.125) inda daga bisani aka cike musu sauran naira biliyan biyu da miliyan dari biyar (N2.5bn) a matsayin kudin siyo tankunan yaki da suka mika ma ofishin NSA a watan Afrilun 2014.

Amma dai mai shari’a Gabriel Kolawole ya dage sauraron karar zuwa 21 ga watan Naris don yanke hukuncin ko za’a iya karbar shaidan a matsayin sahihi kamar yadda lauyoyin wanda ake kara Ernest Nwoye, Afam Osigwe, M Ajara da Nureini Jimoh suka bukata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel