Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba

Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba

– Kungiyar Bayern Munich ta kara tarwatsa Arsenal a Gasar Champions League

– Bayern Munich ta dada durawa Arsenal ci 5-1

– An dai fatattaki Arsenal a gasar nahiyar da ci 10-2

Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba

Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba

Kungiyar Bayern Munich ta kara ladabtar da Arsenal a gasar zakarun nahiyar Turai. Bayern Munich dai ta kuma zubawa Arsenal ci 5-1 kamar yadda aka tashi a wancan karo a Jamus. Yanzu dai an kora Arsenal daga gasar da kwallaye har 10.

‘Yan wasa Lewandowski da Vidal da Arjen Robben suna cikin wadanda suka leka ragar Arsenal din. Dan wasan Arsenal ya karbi jan kati a wasan yayin da Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo guda tun da fari.

KU KARANTA: Ka ji inda aka kama 'Yan Sakandare

Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba

Arsenal ta sha jibga

Haka kuma Napoli ta sha kashi a hannun zakaru Real Madrid da ci 3-1. Shi ma kuma dai haka aka tashi a zagayen farkon kamar wasan Bayern da Arsenal. Real dai tayi waje da Napoli da kwallaye 6-2. Kyaftin Sergio Ramos ne ya jefa kwallaye biyu sai kuma Morata ya kammala aikin bayan dan wasa Mertens ya tsokano mai ‘ya ‘ya.

Shekara 7 kenan ana kora Arsenal daga gasar UEFA Champions League a wannan mataki sai dai wannan karo an yi wa Arsenal din wankin babban bargo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel