‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

A wani nazari da Jaridar Daily Trust tayi mun fara kawo maku jerin ‘yan siyasan da ke iya tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa na 2019. Mun kawo wasu daga ciki, akwai Rabi’u Kwankwaso, Bukola Saraki, Sule Lamido, dsr. Yanzu haka ga cigaba nan:

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

Aminu Waziri Tambuwal

Tsohon kakakin Majalisa kuma Gwamnan Jihar Sokoto na da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa. Yayi yunkurin tsayawa takarar a wancan karo sai kuma ya janye daga baya. Tambuwal yayi kokarin dora Yakubu Dogara a kujerar sa duk cikin siyasar, sai dai Yarbawa ba za su yafe masa ba.

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

KU KARANTA: Za a hana Musulmai shiga Amurka

Ahmed Muhammad Makarfi

Ahmed Makarfi ya mulki Jihar Kaduna daga shekarar 1999 har zuwa 2007, tun daga nan kuma ya wuce Majalisa har 2015 inda ya sha kasa hannun APC. Makarfi wanda yake kokowar kujerar PDP da Ali Modu Sheriff yana cikin masu harin kujerar shugaban kasa. Ana masa kallon mutum mai saukin kai mara kuma zafin ra’ayi.

KU KARANTA: Masu shirin kawowa Buhari cikas a zabe mai zuwa

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

Nasir El-Eufa’i

Malam El-Rufa’i wanda shi ne Gwamnan Jihar Kaduna a yanzu yana iya neman kujerar nan muddin har shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba. Ana tunani Nasir El-Rufa’i zai iya samun kujerar shugaban kasa ko Mataimakin sa nan gaba ganin yadda siyasar ke kadawa.

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2019 II

[Za mu cigaba da kawo maku sauran jerin nan gaba]

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel