Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ranstar da mai shari’a Walter Onnoghen a matsayin alkalin alkalai na 17.

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Onnoghen yayi rantsuwar kama aiki

Anyi taron rantsarwar ne da misalin karfe 9 na safiyar Talata 7 ga watan Maris a dakin taro na majalisar zartarwa dake fadar shugaban kasa, Aso Villa. Bugu da kari an nada ma Onnoghen lambar girmamawa na Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).

KU KARANTA: Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

A satin data gabata ne majalisar dattawa ta tabbatar da sunan mai shari’a Onnoghen kamar yadda mukaddashin shugaban kasa ya bukata bayan aikawa kare wa’adin rikon kwarya da yayi wanda shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya nada shi tun bayan da tsohon alkalin alkalai Mahmud Muhammad yayi murabus.

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin alƙalin alƙalai na 17

Yayin dayake jawabi bayan rantsuwar tasa, mai shari’a Onnoghen ya gode ma shugaba Buhari tare da dukkanin al’ummar kasar dangane da daman da aka ba shi. Shima ya nanata bukatar cin gashin kai na bangaren alkalanci tare da bin doka sau da kafa.

Shi ko Osinbajo cewa yayi Onnoghen yazo yayin da kasar ke matsanancin hali, inda ya sharwarce shi daya jajirce saboda al’ummar Najeriya da daman a bukatar gaskiya da adalci daga gare shi.

sa’annan ya shaida masa cewa ya kira shugaba Buhari a jiya, kuma ya umarce shi daya mika masa sakon taya murna ga sabon alkalin alkalan.

Ranstar da Onnoghen da aka yi ya sanya shi zama alkalalin alkalai na 17 a kasar nan, kuma mutum na 20 daya hau kujerar nan tun 1914.

Mai shari’a Onnoghen na da shekaru 60, kuma ya tun a shekarar 2005 yake kotun kolin kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel