Buhari na biyan N250,000 ga masu farfaganda 40 don suyi sharhi a shafuka – Farooq Keprogi

Buhari na biyan N250,000 ga masu farfaganda 40 don suyi sharhi a shafuka – Farooq Keprogi

A rashin abun da zai nuna cewa yana nan, tunda an kafa sa ne a kan zamba, gwamnatin Buhari ta kafa bakararren farfaganda, da mutane marasa tunani kan wani aiki.

A cewar Farfesa Farooq Keprogi: "Kamar yadda na nuna a shafina na Facebook, wanda yayi yawo a yanar gizo sannan kuma ya siffanta labarin kasa a kan gwamnatin Buhari, shugaban kasar na da mataimaka 9 a kafofin watsa labarai. Kwarai, 9, ba guda 6 ba kamar yadda ake tunani a baya!

Buhari na biyan N250,000 ga masu farfaganda 40 don suyi sharhi a shafuka – Farooq Keprogi

"Mataimakan na sa sun kasance kamar haka: Femi Adesina (Mataimaki na musamman a kafofin watsa labarai da shafin zumunta); Garba Shehu (Babban mataimaki na musamman, a shafin zumunta da kafofin watsa labarai); Tolu Ogunlesi (Mataimaki na musamman a kafofin zamani); Lauretta Onochie (mataimaki na musamman a shafin zumunta) Sha’aban Sharada (mataimaki na musamman a gurin watsa labarai a shafin zumunta); Naziru Muhammed(mataimaki na musamman a shirin talbijin); Lahadi Aghaeze (mataimaki na musamman a daukar hotuna); sannan Bayo Omoboriowo (mataimaki na musamman/ mai daukar hoton shugaban kasa).

"Har ila yau dukka wadannan mataimakan suma suna da wasu mataimaka. Misali, kwanan nan mataimakin shugaban kasa a kafar watsa labarai a shafin zumunta ya nada “mataimaki na 1 a shafin zumunta.” Lamba “1” din na nuna cewa akwai wasu mataimaka na musamman ga mataimakan shugaban kasa da bamu sani ba tukuna.

"Ya kara da cewa, Amma abu mafi muni shine: "shugaban kasar ma na da wata kungiya na boye da kuma masana’antar farfaganda mai suna Buhari Media Center (BMC), wanda ke biyan magoya bayan yada farfaganda kusan guda 40 wanda aikin su shine shafe, yin barazana da kuma tsorata masu sukar gwamnati da dubban shafuka na jabu a kafofin zumunta. Sannan kuma suna cike bangaren sharhi na kafofin watsa labarai da shafukan karya dauke da sunan mutanen kudu wanda ake masu kallon masoyan Buhari. Ana biyan masu yin wannan aiki na farfaganda naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) a ko wani wata.

"Shi wannan ma’aikata na Buhari Media Center, koda dai da wani suna ake kiranta na nan a unguwar Okonjo-Iweala Drive (kusa da barikin CBN) a Jabi Abuja.

"Lokacin da na fara bayyana wannan farfaganda dake aiki a wajen tsarin da gwamnati ta shirya, an karya cewa babu wani abu makamanci haka. A yanzu wani mai suna Muhammad Labbo wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaba/mai kula da sashin na “Buhari Media Support Group” ya yarda cewa akwai wannan ma’aikata cewa ba sunan ta Buhari Media Center ba, sannan kuma cewa wani mutun mai zaman kansa ne ke daukar nauyin ta.

"Amma wanene wannan mutumin mai zaman kan nasa wanda ke daukar nayin wannan? Menene kudirin sa? Shin an biya su ne don suyi wasan damfara? Shin ramawa ne na wani alfarma daga gwamnatin Buhari? Ko kuma alfarmar sakayya ake nema? Me zai kai wani mutun ga daukar nauyin magoya bayan gwamnati?

"Sannan kuma ya maganan naira miliyan dari (N100m) da ma’aikatar bayanai na Lai Mohammed ta tura don “hulda da masu shafuka” a kasafin kudi na 2017? Su wanene wadannan masu shafukan da gwamnati zatayi “hulda” dasu kan naira miliyan dari (N100m) a wannan lokaci na koma bayan tattalin arziki?"

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel