Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno

Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno

Rikicin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram daya faro tun a shekarar 2009 yayi sanadiyar jama’a da dama, kamar yadda gwamnan jihar Kashim shettima ya bayyana.

Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno
Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno

Gwamna Shettima ya bayyana alkalumman barnan da kungiyar tayi a jihar Borno ne yayi wata kasida daya gabatar a ranar tunawa da tsohon shugaban kasa Janar Murtala Muhammad a ranar 13 ga watan Feburairu bana daya gudana a garin Abuja.

Kashim Shettima yace “Rikicin Boko Haram yayi sanadiyyar kusan mutane dubu dari (100,000) kamar yadda shuwagabannin al’ummomi suka tabbatar mana, mutane miliyan biyu da dubu dari da goma sha hudu ne (2,114,000) suka yi gudun hijira, yayin da yan gudun Hijira mutum dubu dari biyar da talatin da bakwai, da dari takwas da goma sha biyar (537,815) suke zaune a sansanoni daban daban; mutum dubu dari da hamsin da takwas da dari biyu da daya ne ke zaune a sansanonin da gwamnati ta san dasu guda 6, da kuma wasu guda biyu na wucin gadi dake Muna da gidan kwastam dake Maiduguri.

KU KARANTA: Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

“Akwai yan gudun hijira dubu dari uku da saba’in da tara, da dare shida da goma sha hudu a sansanonin dake kauyuka guda 15 da suka hada da Ngala, Monguno, Bama, Banki, Pulka, Gwoza, Sabon Gari. mutane dubu saba’in da uku da dari hudu da hudu kuwa sun tsallaka makwabtan kasashen mu don gudun hijira, yayin da Nijar ke karbar bakuntar mutane 11, 402 sai Kamaru na da 62,002.

“Muna da yawan marayu da suka kai dubu hamsin da biyu da dari uku da goma sha daya (52,311) wadandan basu da kowa basu san kowa ba, sa’annan muna da mata da suka rasa mazajensu su dubu Hamsin da hudu da tari tara da goma sha daya (54,911), mata 9,012 daga cikinsu sun koma garuruwan Ngala, Monguno, Damboa, Gwoza da Dikwa.”

Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno
Kashim tare da marayu

Gwamna Kashim ya cigaba da fadin “Rahoton kwamitin sake rayawa tare da samar da zaman lafiya a Arewa maso gabasa wanda bankin duniya tare da kungiyar kasashen Turai da fadar shugaban kasa duk suka tantance ya tabbatar mana da cewa Boko Haram sun janyo mana asarar sama da dala bilyan 9 a yankin, wanda jihar Borno ke dauke da asara na dala biliyan 6.

“Sama da gidaje 956,453 aka lalata yayin rikicin a dukkanin kananan hukumomin jihar, kwatankwacin kashi 30 kenan na gidajen jihar, haka nan ma an lalata gine ginen gwamnati guda 665 da suka hada da ma’aikatu, hedikwatar kananan hukumomi, gidan yari, ofisoshin yansandan, kamfanoni wutan lantarki duk a jihar Borno.

“Rikicin ya lalata mana azuzuwan karatu guda 5,335 a makarantun Firamari 512 da Sakandari 38, sai makarantun gaba da sakandari guda 2, haka zalika sun lalata mana asibitoci guda 201. An lalata famfunan ruwan famfo dana tuka tuka guda 1,630. Bugu da kari yan Boko haram sun lalata mana wuraren shakatawa, lambuna da kuma sace sama da dabbobi 500,000.

Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno
Dalibai mata a makarantar da Boko Haram ta takona

Daga karshe Gwamna Kashim Shettima ya karkare bayanan alkalumman nasa da cewa:

“Duk abinda na ambata, bana lissafin konekonen kasuwanni, da gonakai da kuma manyan motoci masu fitar da kayan gona kasashen waje.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidyon bayani kan Boko Haram

Asali: Legit.ng

Online view pixel