Gwamnatin Kano ta dauki ma'aikatan haraji 765 ta kuduri aniyyar tara naira biliyan 10 duk wata a 2018

Gwamnatin Kano ta dauki ma'aikatan haraji 765 ta kuduri aniyyar tara naira biliyan 10 duk wata a 2018

-Gwamnatin jihar Kano ta dauke ma'aikatan tattara haraji na su 765 domin taimaka mata wajen tattara haraji a jihar

-Gwamnan jihar ya kuduri aniyar tara kudin shiga da ya kai Naira biliyan 10 a duk wata a shekarar 2018 mai kamawa a cewar kwamishinan kudi na jihar

Gwamnatin Kano ta dauki ma'aikatan haraji 765 ta kuduri aniyyar tara naira biliyan 10 duk wata a 2018

Gwamnatin Kano ta dauki ma'aikatan haraji 765 ta kuduri aniyyar tara naira biliyan 10 duk wata a 2018

Kwamishinan kudi, Kabiru Dandago ne ya bayyana haka ranar Litinin 6 ga watan Maris shekarar 2017 a wajen wani taron mika takardun daukar aiki ga ma'aikatan hukumar tara kudin harajin na jihar watau KIRS a gidan gwamnati.

A cewar Dandago, hukumar ta KIRS ta kuduri aniyyar tara naira biliyan 5 zuwa karshen 2017, inda ya bukaci sabbin ma'aikatan da su zage dantse su fuskanci babban kalubalen da ke gabansu na tara kudi duk wata

Ya ci gaba da fadawa sabbin ma'aikatan cewa, albashinsu ya dogara ne kan harajin da su ka tara tun da hukumar na cin gashin kanta ne yanzu.

Sannan ya bukacesu da su tabbatar da abin da ake tsammani daga garesu don samar da kudaden shiga ga jihar da kuma walwalarsu.

"Muna so mu tara Naira biliyan 5 duk wata a wannan shekara. 2018 kuma Naira biliyan 10, saboda haka ku zage dantse don wannan babban kalubale da ke gabanku". cewar Dandago.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, ya bayyana yadda za su samar da wani yanayin aiki da zai bayara da dama ga sabbin ma'aikatan su cimma kudurinsu.

Ganduje ya kuma bukacesu da su jajirce kan aikinsu, ya na mai kira ga jama'a da su yi kokarin biyan haraji don ba wa gwamnati damar gudanar da ayyukan ci gaba ga jama'a.

Gwamnan ya yabawa KIRS bisa canjan tsarin hukumar ta yadda ingancinta zai dace da na kasa da kasa. Ya ce canjin ya zo dai dai da manufar gwamnati ta ci gaba.

A jawabinsa tun da farko, shugaban hukumar ta KIRS Sani Dambo ya ce, daukar ma'aikata na bangare na matakan da ya dauka don kawo gyara ga sha'anin tara kudaden shiga a kokarin mayar da Kano mai dogaro da kanta.

"KIRS na matukar bukatar canja Kano don tsira daga mashassharar tattalin arziki da a ke ciki, shi ya sa mu ka dauki ma'aikata maza da mata 765," cewar Mista Dambo.

"Ya mai girma gwamna , ina baka tabbaci cewa wadannan ma'aikata da mu ka dauka za su tabbatar da mafarkinka na mayar da Kano cibiyar harajin Arewacin Najeriya."

Tun hawansa karagar mulki a Kano gwamna Ganduje ya mayar da hankali wajen tara kudin haraji don samun gudara da ayyukan raya kasa a inda ya gayyato wasu kamfanonin kwararru su 9 domin fitar da tsarin yin hakan.

Ga hoton bidiyon zanga-zangar nuna goyon bayan Buhari da aka gudanar a jihar kwanakin baya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel