Atiku yayi kira ga sake fasalin al’amuran Najeriya

Atiku yayi kira ga sake fasalin al’amuran Najeriya

- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya shawarci Najeriya da ta koma jumhuriyyar gaskiya

- Atiku yace tsarin da Najeriya ke ciki a yanzu yasa kasar ta durkushe ta fannin tattalin arziki kuma baya aiki ga yan kasa sosai

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya shawarci Najeriya da ta koma zuwa ga jumhuriyyar gaskiya don ceto tsarin gwamnatin kasar daga durkushewa.

Atiku wanda yayi wannan sanarwan a jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, jihar Osun, yace a tsarin jumhuriyyar gaskiya, gwamnatin tarayya na bukatar ministoci kalilan kamar yadda sashin tarayyan zasu kula da al’amurran su, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Atiku yayi kira ga sake fasalin al’amuran Najeriya

Atiku ya ce: “Muna da gwamnati dake ba da iko ga gwamnatin tsakiya yayinda take barin rukunin tarayya ba tare da komai ba.

Ana iya kiran tsarin da ake ciki a yanzu da jumhuriyya da ta karkata guri daya.

Dan siyasan, da ake ta yada jita-jitan cewa yana da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019, yace tsarin da Najeriya ke kai a yanzu yasa kasar ta gaza ta fanin tattalin arziki kuma bata bauta way an kasar yadda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Likitoci sun ki ba shugaban kasa Buhari takardan sallama daga asibiti

“Sake fasalin al’amuran jumhuriyyar mu ba wai barazana bane ga hadin kan mu.

“Gwamnatin tarayya bata da wani hujja na samun ma’aikatar noma da lafiya; kawai zasu samu kungiya ne da zasu dunga kula da ma’aikatan. Amma a maimakon haka sunje sun nada ministoci.”

“Menene ruwan gwamnatin tarayya da samun wani ministan lafiya da ministan noma?”

Me yasa muke da hanyoyin tarayya a dukka fadin kasar amma ba’a kula da su? Me yasa muke da asibitocin gwamnatin tarayya da makarantu a dukka fadin kasar amma basu fi na jihar su ba?"

Abubakar ya kuma zargi tsohon ubangidansa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kin amincewa da daya daga cikin shawaransa a ayyukan mulki.

A yau tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da shugaban APC ta kasa, John Oyegun na cikin manyan masu fada a ji da suka je Makurdi don halartan nada farfesa James Ayatse a matsayin sarkin Tiv na 5.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel