Likitoci sun ki ba shugaban kasa Buhari takardan sallama daga asibiti

Likitoci sun ki ba shugaban kasa Buhari takardan sallama daga asibiti

- An dakatar da dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari Najeriya a mintunan karshe na daren ranar Lahadi, 5 ga watan Maris

- Hakan ta kasance ne saboda likitoci na ganin baiyi karfin da zai dawo gida ba

- Hakan ya faru duk da matsa lambar da mambobin dake kewaye da shugaban kasa ke yi

Wani rahoto daga Sahara Reporters ya nuna cewa an dakatar da dawowar shugaban kasa Buhari gida Najeriya a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Maris.

Likitoci sun ki ba shugaban kasa Buhari takardan sallama daga asibiti

A cewar rahoton, likitocin shugaban kasa na ganin baiyi isashen lafiyar da zai dawo gida ba duk da matsin lambar da mambobin da ke kewaye da shi ke yi.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Kiran da Buhari yayi ma Osinbajo ya dakatar da tattaunawa a Benin

Rahoton ya nuna cewa wani majiya da ba’a ambaci sunansa ba daga fadar shugaban kasa yace ana matsananciyar son ganin an dawo da shugaban kasa wanda har ya kai ga an tura wani shakikin makusancinsa zuwa birnin Landan a ranar Juma’a, 3 ga watan Maris tare da babban jirgin shugaban kasa, wani Boeing Business Jet 737 wanda aka sani da “Airforce 001.”

Shirinsu shine su dawo dashi Abuja kafin a kulle filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport a ranar Laraba, 9 ga watan Maris.

A hakan ne, aka dawo da karamin jirgin shugaban kasa wanda ya kai shugaba Buhari birnin Landan zuwa Abuja a wannan ranar yayinda aka tura babban jirgi zuwa Landan tare da sababbin matukan jirgi.

Dawowar dan’uwan shugaban kasa, Mamman Daura da kuma daya daga cikin ‘ya’yanshi mata, a makon da ya gabata yasa ana ta tunanin shugaban kasa Buhari zai dawo a daren ranar Lahadi.

Amma likitocin shugaban kasa Buhari sun ki bashi takardan sallama daga asibiti da zai bashi damar dawowa.

A halin yanzu, shugaban kasa Buhari na ta kiraye-kirayen waya zuwa da shugabannin gida da na waje yayinda yake samun kulawar likita a Landan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel