Gwamna Ayo Fayose ya kara dura kan Obasanjo

Gwamna Ayo Fayose ya kara dura kan Obasanjo

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya kara yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta-tas! Fayose ya fadi wani abu da ya faru tsakanin su da tsohon shugaban kasar a baya.

Yayi abin da ya saba: Ka ji abin da Fayose ya fada game da Obasanjo?

Yayi abin da ya saba: Ka ji abin da Fayose ya fada game da Obasanjo?

Gwamna Ayo Fayose ya fallasa yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tilasta masu hada kudi domin gina dakin karatun sa. Gwamna Fayose yace da karfi da yaji Obasanjo ya karbi Naira miliyan 10 domin ginin dakin karatun sa.

Fayose yace shi fa bai yarda ba, don haka kurum Obasanjo ya maido masa kudin sa da suka bada a baya. Gwamna Fayose yace yanzu kudin har sun karu don kuwa riba ta shiga. Ayo Fayose yayi wannan bayani ne a Jiya Litinin A Birnin Ado-Ekiti wajen wani taro.

KU KARANTA: Obasanjo ya gina dakin ibada domin Musulmai

Ayo Fayose ya bayyana cewa Gwamnoni ne suka hadawa Obasanjo Naira miliyan 10 a shekarar 2005 domin gina dakin karatun sa wanda aka kammala kuma aka kaddamar kwanan nan lokacin da Obasanjo ya cika shekaru 80.

Kwanaki dai Gwamna Ayo Fayose ya fadawa Jaridar Sun cewa babu wanda ya san Obasanjo a Najeriya irin sa don tsohon yaron sa ne shi a baya. Fayose yace tuni ma gara Jama’a su daina daukar kalaman tsohon shugaban da muhimmanci don suna kurum yake nema.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel