An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu

An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu

Wani daga cikin manyan Jam’iyyar APC ya gargadi Ministan sufuri na kasar nan Rotimi Amaechi inda yace ya daina shiga harkokin Jam’iyyar APC na wasu Jihohi ya ji da aikin gaban sa.

An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu

An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu a APC

Wani daga cikin ‘ya ‘yan Jam’iyyar APC a Jihar Kuros-Riba Utum Eteng ya gargadi Ministan Buhari watau Rotimi Amaechi da ya rabu da sha’anin wasu Jihohi ya ji da aikin da ke gaban sa na Ministan sufurin kasar.

Utum Eteng yace Rotimi Amaechi na jefa hannuwan sa inda ba su dace ba don haka ya gargade sa. Eteng yace tsohon Gwamnan na Jihar Ribas na ta kokarin kakabawa mutanen Kuros-Riba mutanen da ya ga dama a Jam’iyya.

KU KARANTA: Shugabannin Majalisa sun shiga uku

An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu

An gargadi Amaechi ya daina shiga sharo ba shanu

Mista Utum Eteng yace Amaechi ya tsaya kan harkokin Jihar sa ta Ribas kamar yadda muka samu labari jiya. Utum Eteng yace tuni dai har ya rubuta wasika ga shugaban Jam’iyyar da kuma shugaban kasa domin a dawo da Amaechi cikin hayyacin sa.

A PDP kuma Shugaban Jam’iyyar ta PDP Ali Modu Sheriff ya sha alwashin hana kafa wata sabuwar Jam’iyya karkashin PDP din. Da alamu dai bangaren su Sanata Makarfi suna shirin kafa wata sabuwar Jam’iyya mai suna APDP.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel