Trump ya kara kafa wata sabuwar doka domin baki

Trump ya kara kafa wata sabuwar doka domin baki

– Shugaban Kasar Amurka ya kara kawo wata doka da za ta hana ‘yan wasu kasashe shiga kasar Amurka

– Kasashen da ake shirin haramtawa shiga Amurka dai duk na Musulmai ne

– A baya dai Trump yayi ta gamuwa da tasgaro

Trump ya kara kafa wata sabuwar doka domin baki

Trump ya kara kafa wata sabuwar doka domin baki

A jiya Litinin ne shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannu a wata doka da za ta hana wasu ‘yan kasashen Musulmai shigowa cikin kasar Amurka. A baya dai shugaban kasa Donald Trump yayi wannan yunkuri sai dai ya gamu da cikas daga kotun kasar.

A dokar za a hana bada takardan shiga Amurka ga wasu kasashe wanda na Musulmai ne. Kasashen dai sune: Libiya, Siriya, Iran, Somaliya, Sudan da kuma kasar Yemen. Sai dai wannan karo an cire kasar Iraki daga jerin kasashen.

KU KARANTA: Abin da ya faru tsakanin Wenger da Sanchez

Haka kuma kasar Amurka za ta dakatar da shirin ta na karbar baki na watanni biyu. Kuma dai Trump ya rage yawan ‘yan gudun hijiran da ke iya shigowa Amurka daga fiye da 110, 000 zuwa 50,000 kacal a shekara. Ana dai sa ran wannan doka ba za ta gamu da wani tasgaro ba.

A baya dai shugaba Donald Trump ya hana Kasashe 6 shiga Amurka na watanni hudu yayin da ya kuma ya haramtawa ‘Yan Kasar Siriya shigowa Amurkar har abada. Wata Kotu da ke Brooklyn ce ta hana a dabbaga wannan doka ta sabon shugaban Kasa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel