Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya danganta halin matsin tattalin arziki da kasar Najeriya ke fuskanta da halin almubazzanranci da tsofaffin gwamnoni suka nuna.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a karshen makon data gabata yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, cikin shagulgulan murnan cikarsa shekaru 80 a rayuwa.

Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

A cikin hirar, Obasanjo ya bayyana cewar ya hango za’a shigo wannan halin karayar tattalin arziki da ake fama da shi bayan ya karanci gwamnoni da suka gabata wadaka kawai suke yi da kudaden asusun jihohinsu.

KU KARANTA: Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

Yace: “A zamanin dana zama shugaban kasa, farashin mai na tsakanin dala 8 zuwa 9 ne, sakamakon haka bama iya cika kasafin kudin mu. Don haka tattalin arzikin kasar na ta yin kwan gaba kwan baya.

“Don haka ne muka fara neman hanyoyin rage kashe kudade da nemo sabbin hanyoyin tara kudade, daga nan sai na fara rokan kasashen duniya da su yafe mana bashin da suke bin mu, bayan an yafe mana basukan ne, sai muka fara siyar da mai, muna adana kudaden.

“Amma a wancan lokaci sai gwamnonin suka basu yarda ba, amma na jajirce nima ban yarda a kashe kudaden gaba daya ba, lallai sai an adana wasu daga ciki, haka ne ya sa muka samar da asusun rarar man fetur.

“Lokaci zuwa lokaci sai gwamnoni su zo suna tambayata ina kason kudin su, tun da ai namu duka ne, amam duk da haka na ki, na nace sai an adana kudin nan. amma da lokacin kashe kudin yayi sai suka almubazzantar da kudaden gaba daya, wannan ne ya shigar damu halin da muke ciki.” Inji Obasanjo

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel