Kungiyar MASSOB na shirin tada rikici a Najeriya idan har…

Kungiyar MASSOB na shirin tada rikici a Najeriya idan har…

– Kungiyar MASSOB tayi kira a saki Nnamdi Kanu

– MASSOB tace idan har ba a saki Nnamdi Kanu ba za a ga tashin hankali

– Nnamdi Kanu ya dade dai yana tsare a gidan yari

Kungiyar MASSOB na shirin tada rikici a Najeriya idan har…

Nnamdi Kanu na daure har yanzu

Kungiyar MASSOB ta shirya kawowa Najeriya cikas idan har ba a saki Nnamadi Kanu ba. Kungiyar da ke goyon-bayan Kasar Biafra ta ba da mako guda kacal domin a saki Kanu wanda yake a tsare na tsawon lokaci.

Kungiyar MASSOB mai fafautukar nemin Kasar Biafra mai ‘yancin-kai ta ce idan har ba a saki Nnamdi Kanu daga gidan kaso ba za su tsaida Najeriya cak. MASSOB din tace za ta shiga zanga-zanga mai uwa da wabe ne a fadin kasar kamar yadda aka taba yi a kasashen India, Ghana da Amurka.

KU KARANTA: Buhari ya kira Osinbajo a waya

Kungiyar tace hankali ba zai kwanta ba idan har ba a saki shugaban na Kungiyar IPOB ba Nnamdi Kanu wanda ya fi shekara a tsare. Kungiyar MASSOB mai neman kasar Biyafara tace za ta kama shugabannin kasar Ibo da laifi idan har ba a saki Kanu ba cikin wannan makon.

Shugaba Buhari ya taba fadawa masu aikin hidimar kasar cewa, su sanar da mutanen su babu wata maganar Biyafara, a manta da ita! Buhari yace a lokacin yakin ba-sasa yana kwamanda Soji, ya taka kafa-ya-kafa tun daga Arewa har can kasar kudu domin Najeriya ta zauna daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Biyafara suna zanga-zanga a Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel