Majalisa ta bankado wata mahaukaciyar badakala a NNPC

Majalisa ta bankado wata mahaukaciyar badakala a NNPC

Majalisar Dattawa ta bankado wata mahaukaciyar badakala a bangaren man fetur na kasar. Majalisar tace ta gano cewa manyan ma’aikatan kamfanin NNPC na kasa sun sace sama da Naira tiriliyan 10.

Tashin hankali: Majalisa ta bankado wata badakala a NNPC

Tashin hankali: Majalisa ta bankado wata badakala a NNPC

Majalisar Dattawa tace ta gano cewa an sace sama da tiriliyan 10 cikin shekaru 10 na man fetur a Najeriya. Majalisar tace wasu manyan ma’aikatan NNPC ne suka yi gaba da wadannan mahauktan kudi tare da hadin-kan ‘yan kasuwa.

Majalisar tace an saci wadannan kudi ne tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016. Kwanan nan dai Kwamitin man fetur da gas na Majalisar Dattawa za su fara binciken kamfunan mai da kuma bangarorin Gwamnati.

KU KARANTA: Ka ji abin da wata kishiyar uwa tayi?

Tashin hankali: Majalisa ta bankado wata badakala a NNPC

Tashin hankali: Majalisa ta bankado wata badakala a NNPC

Jaridar Vanguard dai tace kwamitin na da goyon bayan shugaban majalisar da ma shugaban kasa. Ana kuma sa ran za a hukunta wadanda aka samu da rashin gaskiya. Wadannan kudi da aka sace dai sun isa kasar kashewa na shekaru har biyu. Sanata Marafa wanda shine shugaban wani kwamitin yace ta hanyar tallafin mai ake sace wannan kudi.

Ita kan ta majalisar ana ta inda-inda don kuwa ana gudanar da harkokin cikin majalisa ne ba tare da kowa ya san abin da ke faruwa ba; kama daga kudin da ake rabawa ga ‘yan majalisu domin su yi aiki a yankin su zuwa sauran harkoki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel